About Sales Department

Introduction: This department is created to handle the sales of the company's products and services to customers all over the globe. The department is usually the first point of contact with the customers and therefore our hands are always stretched to welcome you to Gwani Software. The department is headed by Malam Muhammad Idris Alhaji Danbaba who is the director sales and humbly assited by Malam Murtala Muhammad the sales secretary together with other hardworking staff and you for your patronage the department came to where it is.

Barka da isowa sashen saye da sayarwan Kamfani

Gabatarwa Wannan sashe na saye da sayarwa an assasa ta ne don gudanar da saye da sayar da hajojin kamfanin Gwani Software ga masu bukatunsu. Mun kasance zauren farko ga duk wani mai son zuwa Gwani SOftware. Shugaban wannan sashe shine Malam Muhammad Idris Alhaji Danbaba daraktan saye da sayarwa, Malam Murtala Muhammad shine ke agaza masa a matsayinsa na sakataren saye da sayarwa. Wannan kamfani ta kai wannan matsayi da take yanzu da shugabancin waɗannan shuwagabanni nata da ƙwazon ma'aikatanta tare da gudumuwar da kuke bayar wajen sayen hajojinmu.

                                                                                
                                   Mal. Muhammad                                                    Mal. Murtala

Za ku iya mallakan akwatin aika saƙon sms ga duk wanda kuke so a kan Naira huɗu kacal zuwa wayar salula. Zaku iya sanar da mitin ko zama ga 'yan ƙungiyanku, bayanin zuba kuɗi ko cire shi a banki, sanar da iyayen yara canjin ranar dawowa makaranta, sanar da ɗaurin aure ko suna, tallace-tallacen hajojinku, gaishe-gaishenku da sauransu. Kar ku bar wannan babban daman ya shige ku, hamzarta ka cike fom din samun wannan dama, sai a tsaburi alamarta da ke gefen hagu na wannan shafin. Kar a manta sayen nagari mai da kuɗi gida.