Kowa ya bar gida, gida ...

Ƙirƙiro Kamfanin
Kamfanin Gwani Software ta faro ne cikin ikon Allah bisa nazari da wanda ya ƙirƙiro ta yayi, a ganinsa lokaci yayi da za'a shigo da jama'ar Hausawa da masu sha'awan harshen Hausa cikin fasahar na'ura mai ƙwalƙwalwa. Wannan cigaba kuwa zai iya samu ba tare da wani buƙata koyon harshen nasara ba. Bahaushe da harshensa mai albarka zai iya ƙwarewa har ya zamo gwani cikin fasahar na'ura mai ƙwaƙwalwa. Tun zaman wanda ya ƙirƙiro kamfanin a jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke cikin garin Bauchi, ya fara yunƙuri aiwatar da wannan nazari nasa kuma da Allah ya tofa ma gyaɗansa ruwa sai wannan kamfanin naku ya kankama. Sunan kamfanin "Gwani" na nuna shirin wannan kamfani na mayar da masu karatu da muamala da ita wajen gwanancewa ba tare da wani wahala ba.

Ladubban Harkokinmu
Nagarta:- Mun sa ido don ganin dukkan hajojinmu da ayyukanmu sun dace da buƙatunku don kwalliya ta biya kuɗin subulu haka kuma mun haɗa ƙarfi da ƙarfe don ganin jama'anmu sun sami bajinta cikin harkokin na'ura mai ƙwalƙwalwa.
Gwaninta:- Mun sadauƙar da kanmu don ganin almajiranmu da ɗalibanmu sun yi fice a harkar na'ura mai ƙwaƙwalwa tare da ma'aikatanmu baki ɗaya. Haka kuma hajojinmu sun yi fice a duk yadda ake amfani da su.
Amana:-Muna riƙe da amanar masu hulɗa da mu, almajiranmu da ɗalibanmu don samar musu da abarbaden da su ke buƙata cikin fasahar na'ura mai ƙwalƙwalwa.
Aminta:-Muna iyaka ƙoƙarinmu don tabbatar da cewa jama'armu sun aminta da mu kuma sun aminta da kansu kan duk wani abu da ya shafi na'ura mai ƙwaƙwalwa.
Girmamawa:- Muna girmama ɗabi'u, al'adu da addinan sauran ƙabilu da baƙi, hakan kuma a bayyane yake cikin duk wata mu'amalamar mu.
Kasuwanci:-Mun duƙufa wajen samar da arziki don kanmu, ma'aikatanmu da ƙasanmu; ta hanyar shiga halartacciyar kasuwanci da ta shafi na'ura mai ƙwaƙwalwa.
Mutunta:-Mun ƙuduri niyyan cika muhimman muradun ma'aikatunmu da jama'armu ta haka sai mu samar da kyakkyawan yanayi mai mutunta buƙatun bani Adama daga cikin yanayin aiki da kasuwanci.
Bayyane ya ke:- ƙudurorinmu, ra'ayoyinmu da matsayanmu a bayyane suke ga kowa.
Duƙufa:- A duke muke don kawo cigaban fasahar na'ura mai ƙwaƙwalwa a ƙasarmu Najeriya da garuruwan Hausawa da masu sha'awar harshen Hausa.
Tuntuba:- Kowani ɗan Adam da irin baiwar da Allah ya masa don haka muna na'am da shawarwarin masana akan fagen da Allah ya basu sani a kai; neman irin waɗannan shawarwari ya zama dole a garemu.
Biyan buƙata:- Biyan buƙatanmu a kullum tare yake da biyan buƙatan almajiranmu, ɗalibanmu da masu hulɗar kasuwanci da mu.
Ra'ayinmu:- A kullum masu hulɗa da mu sune kan gaba mu kuma na biye, don kuwa ruwan da ya buge ka shine ruwa.
Nasara:-Nasara a kowani irin aiki daga Allah ya ke, shi muke roƙo ya ba mu nasara a dukkanin ayyukanmu.
Haɗin gwiwa:- Kofa buɗe ta ke kullum don haɗin gwiwa da sauran kamfanoni, haɗin gwiwa mai ma'ana da shi a ka sanmu kuma shirye muke don bada tallafi ga duk wata bincike da ta shafi na'ura mai ƙwaƙwalwa.
Tarbiyya:-Muna tafiya bisa tafarki cike da tarbiyya da ladabi hakan ya sa dole ma'aikatunmu da masu koyarwa cikinmu su zamo masu tarbiyya wajen hulɗa da almajiranmu, ɗalibanmu da masu hulɗan kasuwanci da mu.
Faƙira:-Abin da ya ke mai kyau shi ne namu don kuwa nagari na kowa...
Sayen nagari:-Hajojinmu a kullum nagartar su a fili ya ke.
kyautatawa:-kyautata wa marayu na cikin manyan muraɗunmu.


Mun gode.

ɗaukan aiki Jarraba rabonka

ɗaukan aiki na mucingadi don NYSC da SIWES Jarraba rabonka

ICT solutions for your business.

Conception
Gwani Software was conceived as a dream of its founder, to move the Hausa communities and Hausa speaking people into the realm of Information Technology; achievements and professionalism without the necessity of using or learning foreign languages. A dream, the founder conceived during his undergraduate studies in Abubakar Tafawa Balewa University, Bauchi, that is what gave birth to the company - Gwani Software.
International languages can be IT-driven and Hausa being an international language, can be IT-driven.
Gwani is a Hausa word which mean Expert, the major goal of the company is transforming its trainees and customers to become experts in ICT, and our software to gradually assist human experts in their dealings. This is the principle behind the name of our company.

Our Core Values
Excellence:- We ensure that all our services are excellent and clearly seen as such from any perspective. We channel all resources within our disposal to nurture professionalism in IT that is endowed in our trainees and employees.
Expertise:- Our focal goal remain producing experts and competent IT graduates from our training programmes and producing software that can complement the role of experts in our societies.
Trust:-We uphold the trust put in us by our trainee, customers and clients to give them maximum satisfaction in their IT demands.
Confidence:-We put in place resources to inspire our people to have confidence in our ability and in themselves on any IT engagement.
Respect:- We respect all other languages, culture, ideologies and religions and this is reflected in all our activities.
Business:-We strive to create wealth to our members, employees and our country Nigeria by engaging in lawful IT business.
Human:-We put it on ourselves, responsibility to satisfy the basic needs of our employes and our society and to create a conducive human environment out of working environment.
Transparency:- Our policy objectives, decision and disposition remain transparent and available to all asundry.
Commitment:- We are committed to engineering IT development in Nigeria and Hausa speaking communities.
Consultation:- We believe in human potentials and we respect the opinion of experts in their area of expertise and consultation with such experts is paramount in all our activities.
Satisfaction:- Our satisfaction lies with our trainees, customers and clients' satisfaction and this is our focal goal.
Service:- Our service sees trainees, customers and clients as kings and we are faithful services to the kings.
Success:-Success in any endeavour is with God alone, and He alone we are beseeching to grant it to us in all our endeavours.
Partnership:- Our hands to partnership and friendship with other companies are stretched and opened at all times and building a partnership that works is what we are known with and we fund IT research capable of yielding beneficial result.
Morality:-We abide by standard ethics accepted globally in our activities and interactions and our staff and instructors are all expected to behave morally with their trainees, customers and clients.
Inspiration:-Our inspiration is to do good, be good and accept good.
Quality:-Quality is the language spoken by all our products at all times.
Donation:-We generously donate to the well being of orphans as far as our hands can reach.

Thank You.Vacancy Apply Now

Temporary Career for NYSC and SIWES student